Iran ta yi gargaɗi ga ƙasashen yankin cewa: Yaƙi da Iran ba zai kare ba tare da an hukunta su ba
Iran ta yi wa ƙasashen yankin gargaɗi game da sakamakon barin yankunansu, sararin samaniyarsu da kayayyakin more rayuwa a duk wani aikin soja da ake yi a kanta, tana mai jaddada cewa shiga cikin kasadar soja da ke kai hari kan Iran ba zai tabbatar da tsaron waɗannan ƙasashe ba, sai dai zai haifar da da’irar rashin zaman lafiya.
Kamfanin Dillancin Labaran Mehr na kasar Iran ya hakalto cewa: Barazana da Amurka da Yahudawan Sahayoniyya su ke yi wa Iran, tun daga maganar amfani da manyan bama-bamai zuwa kiraye-kirayen kawo ƙarshen rikicin, sun dawo kan gaba a lissafin soja da siyasa wanda gogewa ta baya ta nuna ba ya tabbatar da cimma burin Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Waɗannan barazanar sun zo ne a daidai lokacin da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke fuskantar matsin lamba na siyasa a cikin gida, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke ƙoƙarin magance tasirin manufofin gwamnatinsa a cikin gida. Wannan yana nuna ƙarfin hali da kuma amfani da abubuwan da ke haifar da rikici waɗanda dole ne a yi la’akari da su yayin nazarin matsayin ɓangarorin biyu.