Iran Ta Gargadi Kasashen Makwabta Kada Su Ba Amurka Dama

iran taja kunnen kasashen makwabta da kada su bari ayi amfani da su wajen kai mata hari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran isma’ila Baqai yayi gargadi a jiya lahadi cewa duk wata kasa da ta bari akayi amfani da ita wajen kai wa jamhuriyar musulunci hari to za ta fuskanci mayar da  martani na daban mai ban mamaki, yace Tehran tana tsammanin kasashen makwabta za su yi riko da kyawawan halayen makwabtaka

Yayi wannan bayani ne a taron manema labarai da ya yi a jiya lahadi  inda yace a wannan yankin musamman wadanda suka mika kayayyakin su ga kasar Amurka da Isra’ila a yakin baya bayan nan ya kamata su sake duba irin abin da suka aikata ,idan Amurka da isra’ila suka sake kai wa iran hari daga kasashensu a nan gaba to ko shakka babu martani da zaa mayar zai banbanta sosai

yace  a lokacin taron babban zauren majalisar dinkin duniya jami’an iran sun gana da kusan dukkan wakilan kasashen yammacin takun fasha, game da kasancewar fira ministan isra’ila a kasar hadaddiyar daular larabawa yayi  gargadin cewa gwamnatin isra’ila na neman haifar da wata sabuwar fitina ce a yankin

Daga karshe yayi kira ga kasashen makwabta da kada su amince a ayi amfanin  da kasashensu ta hanyar da bata dace ba daga bangarorin da basu nuna damuwa game da tsaro da ci gaban yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted