Iran Ta Gargadi Makobta Kan Aiki Da Natanyahu

A dai dai lokacinda labara ya watsu dangane da ziyarar aikin da firay ministan HKI Banyemin Natanyahu ya kai kasar Hadaddiyar daular Larabawa, gwamnatin kasar

A dai dai lokacinda labara ya watsu dangane da ziyarar aikin da firay ministan HKI Banyemin Natanyahu ya kai kasar Hadaddiyar daular Larabawa, gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashe makobta musamman gwamnatin Abudabi kan duk wani hadin kai da makiya saboda cutar da JMI, saboda musibar zata koma kanta ne.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran da kuma Parstoday duk sun nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar na gargadin kasashe makobta kan ziyarar da Natanyahu yake yi a yankin da kuma makirce mikircen da zai kulla da kasashe makobta dangane da rikita zaman lafiya a yankin.

Ma’aikatar da kara da cewa kasashen Larabawa na yankin tekun farisa su yi hattara dangane da hada kai da HKI saboda tada hankali a yankin yammacin Asiya saboda rashin zaman lafiya a yankin zai shafi dukkan kasashen yankin a yayinda yahudawan suke kara rauni da zama saniyar ware a duniya.  Saudia ta kuma kasar Jordan sun musanta ganawa da Natanyahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted