Babbar hedkwatar soji ta kasar iran ta gargardi sojojin Amurka cewa dakarun sojin iran za su dauki mummunan mataki kan jiragen ruwan yakin kasar Amurka matukar Washington ba ta daina ci gaba da kai hare hare a yankin ba
Laftanar kanar Ebrahim zolfiqar kakakin hedkwatar soji ta khatamul ambiya ya fadi a jiya Asabar cewa dakarun sojin kasar iran za su mayar da martani mai tsanani idan sojojin Amurka suka ci gaba da kai hare hare da haifar da rashin tsaro da kuma tsakalar jiragen ruwan kasar iran ko kuma ta ci gaba da kawanya ga dakarun sojin ruwan iran
Ya kara da cewa dakarun kasar iran za su kai hari kan jiragen ruwan Amurka a yankin, mafi muni fiye da a baya matukar Amurka ta ci gaba da daukar wadannan matakai, haka zalika yayi gargadin cewa martanin da dakarun iran za su mayar za su fadada shi matukar Amurka ta nuna kunnen kashi
Wannan gargadin yana zuwa ne bayan da sojojin Amurka suka ce dakarun su sun tsare tanakokin daukar mai guda 3 na kasar iran a tekun fasha da kuma tekun Oman