Assalamu alikum barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Kiran Iran zuwa ga hadin kan malaman addinin ga fada da zalunci da kuma tsokana” a taron sient Petersburg” wanda ni tahir Amin zan karanta.
///..Gwamnatin JMI ta yi kira ga malaman addinai da su fito don yakar zalunci da azzalumai da kuma kawo karshen zalunci.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar iran ya nakalto jakadan JMI a Mosco yana fadar haka a yau Asabar, a taron kasa da kasa ta malaman addinai, karo na biyu wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Saent Petersburg na kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa taron wanda ya sami halattar malamai addinai daban daban, ya kuma sami halattar wasu Jami’an diblomasiyya na wasu kasashe. Tawagar JMI sun hada da Kazem Jalili Jakadan JMI a Mosco wanda shi ma ya gabatar da jawabi a taron da kuma shugaban hukuma mai kula da Al-adu da harkokin sadarwa ta musulunci na kasar Iran Hujjatul Islam Muhammad Mahdi Imanipoor.
Har’ila yau taron ya sami halartar shugaban hukumar kusanto da mazhabobin musulunci (shia da sunna) na kasar Iran Hujjatul Islam Hamid Shahriyari. Sakon ya kara da cewa lokaci yayi da musulmi da kuma masu rajin kare hakkin bil’adama a duniya su tashi don kare al-ummar Falasdinu musamman wadanda suke gaza.
Ya kara da lokaci yayi wanda musulmi da masu rajin kare hakkin bil’adama a duniya da shuwagabannin kasashensu su fara aiki a fili don kubutar da al-ummar Falasdinu daga mamayar da akewa kasarsu, saboda har yanzun babu wani al-amari da ya fi al-amarin Falasdinawa a duniya.
Shahriyari ya kara da cewa yakin Ramadan wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa JMI, wanda yake cika watanni 6 da faraway, wani babban darasi ne ga dukkan musulmi, da kuma masu rajin kare hakkin bil’adama a duniya. Ya ce saboda jajircewar JMI kasashe masu girman kai, wadanda suke son ganin bayan JMI, sun fara damuwa kan inda wannan yakin zai kaisu, musamman a dai dai lokacinda basu da wata kasa wacce zata taimaka masu a wannan yankin.
Ya ce Iran mai karfi, ta zama babbar kasa abin koyi ga dukkan kasashen da ake zalunta, ko kasashen musulmi a gwagwarmayarta da kasashe azzalu mai a duniya. Wadanda karfinsu damisa ne ta takarda. Ku yi tawakkalu ga All..ku dogara da shi. Tare da wannan Iran ta zama barazana ga Amurka a yankin yammacin Asia.
A nashi bangaren shugaban hukumar kusanto da mazhabobin musulmi (shia da sunnah’) Hujjatul Islam Muhammad Mahdi Imanipoor ya ce: Amurka tana son a cikin mako guda ta wargaza gwamnatin JMI ta kuma mamaye kasar, kuma da wannan dalilin ne suka fara da kai Jagorammu ga shahada, kafin haka da kuma bayansa sun kashe masanammu da Jami’an gwamnati da manya manyan jami’an sojojin kasar.
Wannan mummunan tunaninta ya zama kamar rubutu kan ruwa, sun zama kamar mafarki garesu. Fitowar mutane a kan titunan biranen kasar Iran, da fafatawar jami’an tsaron su da makiya da kuma yanda Jami’an diblomasiyyar kasar suka jajirce, a duk lokacin yakin, ya sanya suka zama abin buga misali da kuma darasi ga musulmi ga kuma duk masu son kare kansu daga azzalumai a duniya.
Har’ila yau wannan jajircewar ta yi zafi wa gwamnatin Donal Trump na Amurka da kuma HKI da kawayenta.
Shahriyari ya ce: All..T ya bamu nasara a kan makiyammu, sannan sunan Jagora Shahidimmu Imam sayyid Aliyul Khaminae(q) ya wanzu bayansa, musamman bayan da dansa Aya. Sayyid Mojtaba Khaminaei ya gajeshi, a matsayin shugaban masu gwagwarmaya a Iran ga kuma sauran masu gwagwarmaya a duniya.
Yace saboda haka, a halin yanzu ta bayyana ga duniya gaba daya, kan cewa Amurka ta yi rauni, har ya kai ga ba zata iya ci gaba da yaki da JMI ba.
Sai kuma jakadan Iran a Mosco Kazem Jalali wanda a jawabinsa a taron ya ce: Yakamata malaman addini su tashi su koyawa matasa, kishin addini da kuma tarbiyar fada da azzalumai don kare mutuncinsu da kuma addininsu a duk lokacinda hakan ya zama dole.
Jalali ya ce, idan mun koma yakin duniya na biyu, zamu ga cewa mutanen birnin Sient Petersbuge na daga cikin mutane da suka yi gwagwarmaya da azzalumai zamaninsu a lokacin yaki har sai da suka kori makiya.
Yace a yau wannan gwagwarmayan da kuma jajircewar ta tabbata a kasar Iran kasar da nake wakilta a Mosco. Tare da wannan ya kammala da cewa, Tehran da Mosco zasu ci gaba da kara kyautata dankon zumunci a tsakaninsu.