Hizbullah Ta Zargi Gwamnatin Labanon Da Nuna Gazawa

kungiyar hizbullah ta zargi gwamnatin labanon da kasa tabuka komai kan hare haren da isra'ila ke kaiwa

Rahotanni da suka fito daga kasar Labanon sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah  ta ce Isra’ila na ci gaba da kai hare hare a kudancin labanon kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4 tare da jikkata wani adadi mai yawa, adadai lokacin da kasashen duniya suka kasa tabuka komai , da kuma gazawar gwamnatin labanon wajen kare kasar

A cikin bayani da ta fitar a jiya Asabar kungiyar hizbullah ta ce isra’ila tana daukar matakin kai hare hare da kashe mutane da rushe- rushe da kuma tada kauyuka da gidajen jama’a, tace gwamnatin isra’ila na kokarin kawar da yankunan da abin ya shafa da kuma lalata yanayin da ake bukata don ci gaba da rayuwa saboda wasu dalali marasa tushe

Haka zalika hizbulla ta kara da cewa hare haren isra’ila na baya bayan nan a kasar labanon ya janyo mutuwar mutane 4 tare da jikkata wasu da dama,amma babu abin da Amurka ta yi sai ma kara nuna goyon bayanta ga siyasar isra’ila, da kuma sukan gwamnatin labanon na kasa ciki alkawuran da ta dauka.

Daga karashe kungiyar tayi tir da matakin da gwamnatin labanon ta dauka na tattaunawa kai tsaye da isra’ila tana cewa ci gaba da kai hare haren isra’ila da kuma rushe rushe a kudancin labanon, yana nuna gazawa wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted