Hukumar shari’a ta kasar iran ta fittar da bayanai game da binciken da ta gudanar kan burabutsan bomb din da kasar Amurka ta yi amfani da shi wajen kai harin kan wajen da ake taron bikin Aure a makon da ya gabata a kudancin kasar iran, kuma ya nuna cewa makamin na kasar Amurka ne.
Shugaban hukumar shari’a ta lardin hurmuzgan dake kudancin kasar ya bayyana cewa burabutsan da aka samu na makamin da Amurka ta yi amfani da shi a harin da takai a 1 ga watan satumba an yi bincike akansa kuma an gano cewa an kerashi ne a kamfanin Raytheon na kasar Amurka
Wannan yana zuwa ne bayan da har yanzu kasar amurka ta ki amincewa da cewa ita ce ta kai harin kan masu bikin Aure a kudancin kasar , wanda iran ta yi tir da shi kuma ta bayyanashi a matsayin babban laifin yaki, yayin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance yace a farkon makonnan, Washington tana gudanar bincike kan hari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5 tare da jikkata adadi mai yawa
Ghahremani yace harin ya bayyana afili yadda ta keta kudurorin Ganeva guda 4, kuma tuni aka tattara bayanai don daukar matakin shariya na cikin gida da kuma na kasa da kasa kan wadanda suka kai hari da kuma masu hannnu wajen safarar bomb din da aka kai harin da shi.