Mutane biyar suka yi shahada sakamakon hare-haren sama da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kudancin Lebanon
Mutane biyar ne suka yi shahada a ranar Juma’a a wani hari da jiragen sama marasa matuka ciki na sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani babur a Nabatieh da kuma wani hari da suka kai kan garin Ramadiyeh, a daidai lokacin da hare-haren sojojin mamayar Isra’ila suke kara kamari a kudanci da gabashin Lebanon, wanda ya kunshi harba manyan bindigogi da kuma bama-bamai. Sojojin mamayar Isra’ila sun bayyana cewa: Suna mayar da martani ne ga harba jiragen sama marasa matuka ciki na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah.
Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ruwaito cewa: Mutane biyar sun mutu, wasu 24 kuma sun jikkata a farkon adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila a yammacin jiya Juma’a a kudanci da gabashin Lebanon.
Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta tabbatar da cewa: Mutane biyu sun mutu lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari kan babur a garin Kfar Rumman a gundumar Nabatieh. Ta kara da cewa wani hari da aka kai kan wani gida a garin Ramadiyeh, a gundumar Tyre, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da kuma jikkata wasu da dama.
Kamfanin dillancin labaran kasar Labanon ya bayar da rahoton cewa, hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai da bama-bamai sun shafi garuruwan da suka hada da Mansouri, Majdal Zoun, Beit al-Sayyad, Beit Leef, Sarbin, Zawtar al-Sharqiya, Mayfadoun, Barashit da kuma Beit Yahoun.