Gwamnatin Nijar ta zargi Faransa da hannu a yunkurin juyin mulki

gwamnatin jamhuriyar niger ta zargi kasar faransa da kitsa mata juyin mulki da bai yi nasara ba

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta zargi Faransa da hannu dumu-dumu wajen tunzura dakarun da suka kai harin tawaye a wani babban sansanin sojin sama na kasar a makon da ya gabata

Wannan zargi ya fito ne a wata sanarwa ta musamman da gwamnatin mulkin sojan kasar ta karanta a gidan talabijin din kasa ranar Juma’a, biyo bayan binciken farko da hukumomi suka gudanar kan lamarin.

Harin dai ya auku ne a ranar 29 ga Agustan da ya gabata, inda wasu sojoji suka auna sansanin sojin sama na 101 da ke kusa da fadar shugaban kasa a birnin Yamai.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, gwamnatin Nijar ta ce tana da hujjoji masu karfi da ke nuna cewa Faransa ce ta shirya tare da taimaka wa yan tawayen ta hanyar amfani da wata hanyar sadarwa ta sirri.

Wannan sabon rikici ya kara ruruta wutar rikici da tsamin dangantaka da ke tsakanin Nijar da tsohuwar ‘uwar gijiyarta Faransa tun bayan juyin mulkin shekarar 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted