Iran ta gargadi Amurka kan barazanar harin bam da Trump ya yi

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin.

Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana.

Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Wakilin na Switzerland ya ba da tabbacin cewa nan take zai isar da sakon Iran ga gwamnatin Amurka.

A ranar Asabar ne Trump ya ce za a kai wa Iran hari idan ba ta kulla yarjejeniya da Amurka ba.

“Idan ba su kulla yarjejeniya ba, za a ji bama-bamai,” in ji shi a wata hira da NBC News. Ya kuma yi barazanar ladabtar da Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments