Iran Ta Ce Kalaman Grossi Shugaban Hukumar IAEA, Sun Sabawa Matsayin Hukumarsa

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce, wata maganar da shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA, Rafael Grossi ya fada, a

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce, wata maganar da shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA, Rafael Grossi ya fada, a baya-bayan nan ya sabawa, tsarin da hukumarsa take tafiya a kansa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi ya na fadar haka a yau Laraba.

Kafin haka dai an nakalto Grossi yana fadawa wata tashar talabijin ta kasar Italiya kan cewa JMI ta kusan kaiwa ga kera makamin nukliya, don haka a halin yanzu yarjeniyar JCPOA ba zai watarda ba, dole ne a sami wani sabon shiri wanda zai sake lalen yadda ake daukar shirin makamashin nukliya na kasar Iran.

Garibabadi ya  na maida martani ga shugaban hukumar ta IAEA a shafinsa na X a ranar litinin, ya kuma kara da cewa ai yakamata shugaban hukumar yayi magana dai-dai da abinda masu binciken hukumarsa suka bayar, ba sabanin ibinda ya tabbata a kasa ba.

Yace duk abinda Grossi ya fada wa wata talabijan ta kasar Italiya, ba shi ne rahoton da masu binciken hukumar suka kaiwa hukumar ba, kuma abinda ya fada kan zato ne kawai ba gaskiya ba.

Ya kuma kammala da cewa, shirin nukliyar kasar Iran ban a kera makaman nukliya bane, sannan hanyoyin kera makaman Nukliya sananne ga ma’aikatar hukumar. Don haka jawabin da gorossi yayi wani kokarine na hana kasashen damar amfani da fasahar nukliya ta zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments