Kakakin gwamnatin Iran ta bayyana shirin Tehran na sake bude ofishin jakadancinta a Damascus, a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen da kasar Siriya ke fuskanta makonni biyu bayan da mayakan Hayat Tahrir al-Sham (HTS) suka kwace mulki da birnin Damascos.
“Hanyarmu ta sake bude ofisoshin jakadancin ta hanyar diflomasiyya ce, kamar yadda aka saba, kuma a shirye muke don hakan,” in ji ta.
Ta kara da cewa “Sun kuma shirya, kuma a halin yanzu muna tattaunawa ta diflomasiya don sake bude ofisoshin jakadancin.”
Bayan da mayakan HTS suka kwace iko da Syria a ranar 8 ga watan Disamba, wanda ya kawo karshen mulkin Bashar al-Assad na tsawon shekaru 24, kasar na ci gaba da fuskantar manyan kalubale ta fuskar kasa da kasa.
Zaman lafiyar kasar Siriya da makomarta na fuskantar kalubale iri daban daban da suka hada da mamayar da Isra’ila ta yi wa kasar, da kuma ci gaba da kasancewar kungiyar mayakan SDF da ke samun goyon bayan Amurka a cikin kasar.