Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi kira ga kungiyar Shanghy wato the Shanghai Cooperation Organization (SCO) da ta samar da banagaren tsaro na hadin guiwa saboda tabbatar da tsaro na yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake halartar taron ministoci na kungiyar a kasar China a jiya Talata. Yace wannan zai taimakawa kungiyar ta kasance zata iya taimakawa kasashen kungiyar a duk lokacinda suka fuskanci matsalar tsaron.
Labarin ya kara da cewa , wannan shi ne taron ministocin harkokin wajen na kungiyar karo na 25TH . inda aka sami wakilai ko ministocin harkokin wajen kasashe 120 wadanda suka sami halattar sa. Banda haka akwai kungiyoyin kasa da kasa da dama sun sami halattan taron. Daga cikinsu akwai kungiyar yan ba ruwammu, wato ‘the Non-Aligned Movement, kungiyar kasashen musulmi OIC, BRICS, da kuma iata shanghai SCO,. Kasashen da kuma kungiyoyin suna bukatar daukar mataki na samar da kudubobi a duniya, sabanin yadda gwamnatin Amurka take so.
Taron zai tattau na kan abubuwan da suke faruwa a duniya a yanzu, musamman matsalar al-ummar Falasdinu. Sannan a gefen taron za’a ci gaba da ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da China. Iran zata gana da dukkan wadannan ministoci da kuma kari. Araghchi ya bada shawarar aiwatar da abubuwa guda 4 daga cikin har da tsaron hadin guiwa tsakanin kasashen kungiyar.