Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar

Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da hare-haren da HKI ta kai helkwatan kungiyar Hamas a Doga, ta kuma kara da cewa wannan wani sako

Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da hare-haren da HKI ta kai helkwatan kungiyar Hamas a Doga, ta kuma kara da cewa wannan wani sako ne ga kasashen yankin na su yi shirin kare yankin ko kuma zasu ga abinda ya fi haka nan gaba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani yan fadar haka a shafinsa na X. Ya kuma kara da cewa: Hare-haren Qatar gargadi ne na bainda zai zo nan gaba.

A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya rubuta a shafinsa na X kan cewa, abinda HKI ta yi a doha baa bin mamaki bane a waje na’ sannan ya mika ta’aziyyarsa ga mutane da gwamnatin kasar Qatar da kuma kungiyar Hamas wacce aka kaiwa hare-haren.

Daga karshe ya bukaci hadin kan musulmi da kuma aiki tare don fuskantar ayyukan ta’addancin HKI. Ya ce JMI a shirye take don shiga duk wani matakin da za’a dauka a kan HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted