Abbas araqci ministan harkokin wajen kasar iran yayi amfani da ganawar da yayi a gefen taron majalisar dinkin duniya a birnin newyork wajen bayyana batutuwan tsaro da kasar Iran ke fuskanta inda yayi ishara da batun tsaro a kan iyakarta da kasar Iraki , kana yayi gargadi ga kasashen yankin da ma kasashen turai game da barin ayi amfani da kasashensu ko kayan aikinsu wajen daukar mataki kan kasar iran
A wata ganawa da ministan tsaron kasar iran yayi da takwarorinsa na kasashen iraki, faransa da jamus a jiya talata sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashensu, da ci gaban da aka samu a yankin da kuma yakin da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar iran
haka zalika a ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar iraki Fuad Hussain dukkan bangarorin biyu sun jaddada game da muhimmanci tabbatar da tsaro a iyakokin kasashensu, da kuma yin aiki da yarjejeniyar da suka cimma akan batun, da kuma daukar mummunan mataki kan yan ta’adda
A ganawarsa da minsitan harkokin wajen kasar Faransa Jean noel barrot da wasu jami’ai guda biyu sun tattaunawa kan dangantakar diflomasiya dake tsakanin kasashensu dama yankin , kuma ya caccaki kasar faransa game da tsoma baki cin harkokin cikin gidan iran, kuma ya bukaci ofishin jakadancinta dake Tehran da ya girmama doka da oda .