Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian ya yi kira ga manyan masu samar da makamashi a duniya da su yi Allah wadai da kuma dakile dabarun Amurka da ke barazana ga dorewar kasuwannin makamashi na duniya.
Da yake jawabi a taron koli na 8 na kasashen da ke fitar da iskar gas na (GECF) a Moscow, shugaban Iran ya jawo hankali kan manyan kalubalen da kasuwannin makamashi na duniya ke fuskanta, yana mai nuna munin illar da hare-haren sojojin kasashen waje ke yi wa zaman lafiyar yankin.
Taron Kasashen da ke fitar da iskar gas ya tattaro manyan kasashen duniya masu samar da iskar gas kuma ya zama dandanli na hadin gwiwa kan ci gaba a kasuwannin iskar gas na duniya.
“Matakan soja da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka dauka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya faru a matakai biyu kuma a tsakiyar tattaunawar siyasa, yana daya daga cikin abubuwan da suka fi damun jama’a da kuma hatsari ga tsaron duniya,” in ji Mr. Pezeshkian a lokacin jawabinsa a taron.
Shugaban Iran ya kuma yi Allah wadai da matakan Washington da ya danganta da na ta’addancin tattalin arziki, musamman ta hanyar sanya takunkumi, toshe hanyoyin jiragen ruwa da na sama a kan Iran, da kuma matsin lamba mai tsanani da ake yi wa wasu kasashe don tilasta musu bin bukatun Amurka ba bisa ka’ida ba.
Da yake mayar da martani kan illar da sojojin kasashen yamma ke yi wa yankin, Mr. Pezeshkian ya jaddada cewa tsoma bakin sojojin Amurka a Tekun Farisa ya kawo cikas ga farashin makamashi, wadatuwarsa, jigilarsa, yayin da kuma yake kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Shugaban na Iran ya yi kira ga kasashen mambobin kungiyar da su karfafa hadin gwiwarsu a fannoni biyu wanda ya shafi “tsarin mulki da gudanarwa”, domin tabbatar da dorewar kasuwa da kuma kara cinikayya, na biyu kuma wanda ya shafi “ayyukan fasaha da injiniya”, da nufin inganta zuba jari tare a fannin iskar gas, daga samarwa zuwa sarrafawa, jigilarsa da kuma amfani da shi.