Mataimakin ministan harkokin wajen kasar a Iran ya gana da shugaban hukumar yan gudun hijira ta MDD, inda ya bukaci karin taimako daga hukumar don kula da miliyoyin yan gudun hijiran Afganisatn a kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Seyed Mohammad Bathaei yana fadar haka a taron kwamitin gudanarwa na hukumar UNHCR karo na 76 a birnin Geneva na kasar Swizland.
Labarin ya kara da cewa Iran tana daga cikin kasashen da suke daukar bakwancin yan gudun hijira daga kasar Afganistan mafi girma a duniya. Rashin zaman lafiya a kasar Afganistan na shekaru fiye da 40 ya maida mutanen kasar da dama yan gudun hijira a kasashen duniya musamman kasashe makobta.
Filippo Grandi shugaban hukumar ta UNHCR ya yabawa kasar Iran a kokarin ta na kula da yan gudun hijiran Afganistan na lokaci mai tsawo sannan ya yi alkawalin kara tallafi ga kasar.