Iran ta sake yin Allah wadai da kame Shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa, Cilia Flores, da Amurka ta yi, tare da bukatar a sake su ba tare da wata wata ba.
A yayin taron manema labarai na mako-mako yau Litinin, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa harin da Amurka ta kai wa Venezuela wani lamari ne mai hatsari wanda ya keta hurumin kasar.
Ya kara da cewa keta dokokin kasa da kasa akai-akai ya kamata ya sa al’ummar duniya su yanke hukuncin cewa, duniya na fuskantar barazanar fadawa cikin rudani da rashin zaman lafiya.
Mai Magana da yayun harkokin wajen kasar ta Iran ya ce sabbin abubuwan da suka faru a Venezuela “suna da matukar hatsari” wanda hakan ya jawo Allah wadai daga kasashe da dama.
” Wannan sabon tsari babu shakka zai haifar da sakamako ga dukkan al’ummar duniya, in ji jami’in na Iran, wanda ya yi imanin cewa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dinkin Duniya, da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suna da alhakin kare ka’idoji da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
A ranar Asabar ne, sojojin Amurka suka abkawa Venezuela da hare hare inda kuma suka yi awon gaba da shugaban Venezuela Nicolás Maduro da matarsa a Caracas kafin su mayar da su New York a matsayin wani bangare na wani matakin soja da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka.
Amurka na tuhumarsu da safarar miyagun kwayoyi.