Iran Ta Bukaci A Kori HKI Daga Kungiyar CICA

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren al-amuran kasa da kasa ya yi kira ga kungiyar CICA wato ‘the Conference on Interaction and Confidence

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a bangaren al-amuran kasa da kasa ya yi kira ga kungiyar CICA wato ‘the Conference on Interaction and Confidence Building Measures in Asia’ ta kori HKI daga kungiyar saboda ita ce musabbibin mafi yawan tashe tashen hankula a yankin yammacin Asia.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Kazem Gharib Abadi yana fadar haka, a taron CICA karo na 7th a birnin Baku babban birnin kasar Azarbaijan a jiya Alhamis.

A jawabinda ya gabatar a taron Gharib A badi ya yi magana ya kuma bayyana matsayin JMI dangane da al-amuran yankin yammacin Asia da kuma na kasa da kasa. Har’ila yau da tsaron yankin da kuma duniya gaba daya.

Yace ana gudanar da wannan taron a bana, a dai dai lokacin da kasashen yankin suke cikin mummunan hali na tsaro tattalin arziki da matsalolin al-adu. Ana gudanar da wannan taron a dai dai lokacinda wasu kasashen suke amfani da karfi a duniya don tursaswa wasu kasashe ra’ayinsu da kuma siyasarsu. Wanda ya kara dagula al-amura da dama a duniya. Haka ma suna amfani da barazana, takunkuman tattalin arziki don tilastawa wasu kasashen bin ra’ayinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted