Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fayyace matsayinta kan tsarin kafa sabuwar gwamnati a kasar Siriya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Baqir Qalibaf da kuma ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi sun bayyana matsayin Iran kan tsarin kafa cikakkiyar sabuwar gwamnati a kasar Siriya ga ministan harkokin wajen kasar Oman Badar al-Busaidi wanda ya ziyarci Tehran fadar mulkin kasar Iran a jiya Litinin.
Zaman lafiya da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, su ne muhimman batutuwan da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gabatar a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Oman Badar al-Busaidi, inda ya jaddada cewa hanyar da Iran take bi a aikace ita ce fadada zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma tsakanin dukkanin kasashen musulmi.
Pezeshkian ya kara jaddada yin kira kan fadada alaka da mu’amala mai karfi tsakanin Iran da masarautar Oman ta fuskar inganta tsaro da zaman lafiya a yankin, bisa la’akari da yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ke amfani da sabanin da ke tsakanin kasashen yankin wajen kai hare-haren wuce gona da iri kansu da cutar da su.