Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana wasu hanyyoyi na warware rikicin kasar Siriya.
Araghchi ya jaddada muhimmancin kiyaye ‘yancin kai, da mutuncin kasar Siriya ta hanyar hadin kan kasa da kuma gudanar da zabe cikin ‘yanci.
Ya kuma yi karin haske kan tasirin rashin zaman lafiya a yankin.
Ministan ka kuma yi Allah wadai da gazawar kasashen duniya na daukar mataki kan Isra’ila, yana mai kwatanta irin ta’asar da ‘yan Nazi suka yi a Jamusa matsayin abinmda Isra’ila ke aikatawa.
Ya kuma yi gargadi game da tsoma baki da kasashe irinsu Amurka da Isra’ila ke yi, wadanda ya ce suna da nufin wargaza tsarin zamantakewar al’ummar kasar Siriya, da ababen more rayuwa na tattalin arziki, da kuma karfin tsaro.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda kungiyoyin ‘yan ta’adda irin su ISIS da Al-Qaeda ke ci gaba da yin amfani da Syria a matsayin sansani.
Araghchi ya bayyana matsayin Iran kan warware rikicin kasar Siriya, yana mai jaddada bukatar gudanar da sahihin zabe a matsayin ginshikin sake gina al’ummar kasar.
Ya kuma bukaci a sanya dukkan al’umma da kabilu cikin wannan tsari.