Iran ta bukaci cibiyoyin ilimi na kasar da su shirya karbar daliban da aka hana su shiga makaranta saboda hijibi.
Mataimakin Shugaban Kasa Na Farko Na Iran Ya Umarci Cibiyoyin Ilimi Na kasar Da Su Saukaka Shiga Ɗaliban Azerbaijan Da Aka Hana Su Zuwa Makaranta bayan matakin hana shiga makaranta da hijabi ya fara aiki.
A cikin wani saƙo da aka wallafa a shafinsa na Twitter, Mohammad Reza Aref ya yaba wa Ma’aikatar Kimiyya kan yadda ta yi maraba da shigar ‘yan matan Azerbaijan sanye da hijabi, waɗanda aka hana su samun ilimi a kasarsu.
Ya kuma yi kira ga Ministan Ilimi da Shugaban Jami’ar Musulunci ta Azad da su ɗauki matakan da suka dace don ba wa ɗaliban Azerbaijan damar ci gaba da karatunsu.
A watan da ya gabata ne, Majalisar Ministocin Azerbaijan ta amince da wani kuduri da ya haramta sanya tufafin da aka bayyana cewa sun saɓa wa ƙa’idar sanya kayan makaranta a ƙa’idar ilimin boko.
Bugu da ƙari, Ma’aikatar Ilimi Ta Azerbaijan ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike don tabbatar da cewa ɗalibai da malamai suna bin wannan sabon matakin.
Kodayake haramcin bai ambaci hijabi a fili ba, bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna cewa ya fi mayar da hankali kan ‘yan mata masu lulluɓi.
Wannan matakin ya kuma haifar da fushi a duk duniya, inda masu amfani da shafukan sada zumunta suka yi Allah wadai da shi a matsayin cin zarafin addini ga al’ummar kasar da galibinsu Musulmi ne