Iran Ta Bada Agajin Gaggawa Ga Pakistan Bayan Ambaliyar Ruwa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu.

Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y ace kasar Iran a shirye take ta bada agaji ta kuma aike da yan kwana-kwana don taimakawa kasar fita daga wannan halin da take ciki.

Shugaban yayi fatan warkewa da sauri ga wadanda suka jikata ko suka ji ciwo a sanadiyyar wannan ambalin ruwa a kasar ta Pakisatn.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jawo ambaliyar ruwa mai yuwa, ya kuma rufe gidaje, ya rusa wasu sannan ya lalata wasu a cikin kasar ta Pakisatan a cikin makon da ya gabata, kuma har yanzun ana ruwa a wasu yankuna a kasar ta Pakisatan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted