Iran Ta Aike Wa MDD Wasika Akan Barazanar Da Trump Ya Yi Mata

Bayan barazana kawo wa Iran hari da shugaban kasar Amurkan Donadl Trump ya yi, jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a MDD, Amir Sa’id Iravani,  ya

Bayan barazana kawo wa Iran hari da shugaban kasar Amurkan Donadl Trump ya yi, jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a MDD, Amir Sa’id Iravani,  ya aike da wasika zuwa ga kwamitin tsaron na MDD da kuma babban magatakardanta  Antonio Guterres yana mai yin  Allawadai  da barazanar, wacce kuma ta sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.”

Jakadan  na jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya yi Allawadai da sabuwar barazanar ta Donald Trump akan  jamhuriyar musulunci ta Iran.

A shekararn jiya Litinin 29/Disamba  2025 ne dai shugaban kasar Amurka ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila da a ciki ya ce:

“Idan har Iran ta ci gaba da gudanar da shirinta na Makamai Masu linzami,to kuwa zan goyi bayan kai mata hari. Idan kuma ta ci gaba da shirinta na Nukiliya, to za mu kai mata hari.”

Jakadan na Iran ya kuma ce; Magana irin wannan tana a matsayin tsokana, da kuma tayar da zaune tsaye, da take dokokin Majalisar Dinkin Duniya ,musamman doka mai lamba ta 2 a karkashin sakin layi na 4 da ta hana amfani da karfi ko yin barazana amfani da karfi akan zaman lafiya na wani yanki, ko kuma akan wata kasa mai ‘yanci.

Jakadan na jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yi Ishara da harin hadin gwiwa na Amurka da ‘yan sahayoniya akan Iran a tsakanin 13 zuwa 24 ga watan Yuni 2025, ya jaddada wajabci a yi Allawadai da shi, haka nan kuma furucin karshe na Amurkan.

Sa’id Iruni ya kara da cewa; A ranar 6 ga watan Nuwamba 2025, shugaban kasar ta Amurka ya fada a fili cewa; Amurka ta shiga cikin hari akan Iran kai  tsaye.

 A karshen ya bukaci a ajice wannan wasikar a matsayin ta tarihi a MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted