Iran: Shirin MGWT 20,000 Na Wutan Lantarki Zai ci gaba

Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Dr Mohammad Islami ya bayyana cewa cibiyar samar da wutan lantarki na Bushar ya zuwa yanzu ta taimaka

Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Dr Mohammad Islami ya bayyana cewa cibiyar samar da wutan lantarki na Bushar ya zuwa yanzu ta taimaka wajen ta taimakawajen hana samuwar ton miliyon 90 guban Cabon a iran saboda wutan lantarki mai tsabta da take samarwa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yanakalato Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Lahadi a wani taron makamashi mai tsabta a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa shahadar dalabai da malaman makarantar shajara Attayyiba 168 a Minab wani al-amari ne da ya zama tabo a goshin Amurka har abada.

Ya ce shahadar yan makarantar Minab da sauran shahidan kallafaffun yake yaken  abu ne wanda Iraniyawa ba zasu taba manta da su ba. Shugaban hukumar y ace fasahar nukliya a kasar Iran kokari ne wanda matasan kasar suka yi Alll..ya basu nasara suka mallake ta. Wannan fasahar ya yi tasiri a rayuwar mutanen Iran a bangarori da dama, daga wutan lantarki mai tsabta zuwa magunguna masu muhimmanci wadanda kasashen yamma suke makonsa sai ga wanada suke so.

Ya ce kasashen yamma musamman kasar Faransa tana samar da kasha 67% na wutan lantarki a kasar tare da amfani da makamashin Nukliya, amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran sun ki su kammala aikin samar da makamashin nukliya a kasar Iran sannan sun hana wani ma ya shigo don kammala shi.

Yace cibiyar makamshin nukliya na Bushar a Iran yana daga cikin cibiyoyin bada wutan lantarko 10 mafi inganci a duniya. Don ta hana yaduwar guban Cabon tun miliyon 90 ya zuwa yanzu a kasar Iran a cikin shekaru 11 da fara aikinta. Sannan hana kona man gas har ton 120 miliyon. Babu gurbatan yanayi ko kadan sannan amince 100%.  Don haka Iran zata ci gaba da aikin samar da wasu karinmegawat 20,000 na da yan shekaru masuzuwa. Daga makamashin yuranium.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted