Ministan tsaron kasar Iran Burgedia Janar Aziz Nasir Zadeh ya bayyana cewa Iran a shirye take ta maida martani mafi tsanani kan makiya idan sun kuskura sun sake takalar kasar da yaki. A wannan makaron makamai zasu yi kisa mai yawa a kan sojojin makiya. Ya ce an kammala dukkan gwaje-gwajen da yakamata a iyawa makaman, kuma a shirye suke suka fara aiki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’in sojan yana cewa idan an fara yin amfani da su makiya zasu fahinci zewa akwai bambanci da wadanda muka yi amfani da su kan HKI a yakin baya-bayan nan, a karfi da kuma fadawa a inda ske son ta fada. Banda haka mutanen zasu yi mamakin wadan nan makaman.
Ya kuma jaddada anniyarsu ta samar da garkuwa daga makaman HKI ta hanyar samar da makamai masu linzamu masu karfi wadanda zasu iya kakkabo makaman HKI ba tare da wani kuskure ba.
Tehran ta bayyana cewa a shirye su faskansu makiya musamman HKI da Amurka tare da wadannan sabbinmakamai masu linzamai wadanda aka girka masu kayakin aikin zamani. Yace Iran a shirye take a yawa da kuma ingancin makamanta da kuma sakonni ko yakin kayakin lantarki na nruwa da na tudu.