Rundunar Sojan Ruwa ta Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta fara wani atisayen soja a gabar tekun kudancin kasar, a mashigar Hormuz.
Atisayen, wanda aka yi wa lakabi da “Smart Control of the Hormuz,” ya fara ne yau Litinin kuma babban kwamandan rundunar IRGC Manjo Janar Mohammad Pakpour ne ke kula da shi kai tsaye.
Aikin atisayen yana da nufin gwada shirye-shiryen rundunar Sojan Ruwa ta IRGC da kuma tunkarar duk wata barazanar tsaro a mashigar Hormuz.
Iran na gudanar da atisayen jiragen ruwa a mashigin na Hormuz yayin da Amurka ta tura dakarun soji zuwa yankin, ciki har da jiragen yaki na F-35, da manyan jiragen ruwa wanda hakan ke kara nuna damuwar fadawa wani rikici a yankin.
Jami’an Amurka sun kuma ce Pentagon za ta aika da wani jirgin ruwa na daukar jiragen sama zuwa yankin, gami da dubban sojoji tare da jiragen yaki ciki har da masu sarrafa kansu.
Da yake jawabi a Fadar White House ranar Juma’a, Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa wani jirgin ruwa na biyu – USS Gerald R Ford – zai bar Caribbean zuwa Gabas ta Tsakiya “nan ba da jimawa ba.”
A ranar Lahadi, Babban Hafsan Hafsoshin Soji Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya gargadi shugaban Amurka game da duk wani rikici da Jamhuriyar Musulunci, yana mai cewa irin wannan matakin zai zama darasi ga Washington.