Iran, Rasha, da China sun yi Allah wadai da Amurka kan haddasa tarzoma a Iran

Kasashen Iran Rasha da kuma China, sun yi tir da Amurka kan ingiza masu zanga zangar data rikide zuwa tarzoma a Iran. Mataimakin Wakilin Iran

Kasashen Iran Rasha da kuma China, sun yi tir da Amurka kan ingiza masu zanga zangar data rikide zuwa tarzoma a Iran.

Mataimakin Wakilin Iran na Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamhossein Darzi, ya soki Amurka sosai a yayin taron gaggawa na Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan tarzomar da kasashen waje suka haddasa a kasar.

M. Darzi ya kira lamarin da “abin kunya” cewa Washington ta mayar da Majalisar Dinkin Duniya “wurin wasan kwaikwayo” ta hanyar zarge-zarge marasa tushe da kuma yunkurin amfani da zanga-zangar lumana a Iran.

Zaman wanda Amurka ta kira, ya maida hankali ne kan zanga-zangar da aka yi kwanan nan a Iran kan matsin tattalin arziki, hauhawar farashin kaya da kuma faduwar darajar kudin kasar.

Zanga-zangar da ta soma cikin lumana ta rikide zuwa tarzoma bayan tsoma bakin Amurka da Isra’ila.

Jakadan Iran ya yi gargadin cewa duk wata barazanar amfani da karfin soja ko tsoma baki a karkashin hujjar kare masu zanga-zanga ya sabawa dokokin ƙasa da ƙasa da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, yana mai kira ga Kwamitin Tsaro da ya yi watsi da irin waɗannan ayyuka.

Shi ma wakilin Rasha na Dindindin a MDD, Vasily Nebenzya, ya ya bayyana kalaman Amurka a matsayin “hadari.”

Ya ce “sojojin waje masu adawa da juna” suna amfani da wannan yanayi don kifar da gwamnati da kuma wargaza Iran a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Ita ma China ya soki barazanar Amurka da shishigi a harkokin cikin gidan Iran.

Beijing ta bukaci dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan su kuma su yi watsi da hanyoyin da za su iya jefa yankin cikin tashin hankali.”

A nata gangare MDD ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan tashin hankali, da kuma guje wa fadawa wani sabon rikici a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted