Iran, Rasha, China sun kuduri aniyar karfafa yarjejeniyar nukiliya

Kasashen Iran, Rasha, da China sun fitar da sanarwar hadin gwiwa ta bangarori uku dangane da yarjejeniyar nukiliyar, inda suka tabbatar da cewa har yanzu

Kasashen Iran, Rasha, da China sun fitar da sanarwar hadin gwiwa ta bangarori uku dangane da yarjejeniyar nukiliyar, inda suka tabbatar da cewa har yanzu tanade-tanaden shirin hadin gwiwa na JCPOA na nan a raye.

Sanarwar ta bayyana cewa, “kasashen ukun ba su yi kasa a gwiwa ba wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar da kuma ci gaba da kare wannan yarjejeniya, tare da ci gaba da jajircewa kan dukkan abubuwan ad suka rataya a kan dukaknin bangarorin yarjejeniyar.”

Sun sake jaddada aniyarsu na yin duk abin da ya dace don farfado da yarjejeniyar.

Kasashen uku sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da matsayar sauran kasashen da abin ya shafa, wato Faransa, Jamus, Birtaniya, da Amurka, saboda zabar wata hanya ta daban dangane da wannan yarjejeniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments