Iran : Pezeshkian Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Joseph Aoun

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya mika sakon taya murna ga Joseph Aoun kan zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasar Labanon, yana

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya mika sakon taya murna ga Joseph Aoun kan zaben da aka yi masa a matsayin shugaban kasar Labanon, yana mai bayyana aniyar Tehran na kara karfafa hadin gwiwa da huldar da ke tsakaninta da Beirut.

Shugaba Pezeshkian ya rubuta a cikin sakon taya murnarsa cewa “Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana bayyana aniyarta na kara karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni.

Shugaban na Iran ya bayyana fatansa na cewa zaben zai kawo kwanciyar hankali a siyasance, da ci gaba da bunkasar tattalin arziki, da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar Lebanon abun kauna.

Joseph Aoun ya lashe kuri’u 99 daga cikin 128 da ‘yan majalisar dokokin Lebanon suka kada inda ya lashe zaben shugaban kasar a zagaye na biyu da aka gudanar a ranar Alhamis.

Zaben dai ya samu goyon bayan kungiyoyin siyasa daban daban da suka hada da ‘yan majalisar Hizbullah da ‘yan adawa.

Wannan ya zo ne a yayin yunkurin majalisar dokokin kasar karo na 13 na neman nada wanda zai gaji Michel Aoun wanda wa’adinsa ya kare a watan Oktoban 2022.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments