Iran, Pakistan, Turkey, Saudia Sun Gudanar Da Taro Tsaro A Tehran

Wakilan kasashen Iran, Pakistan Turkiya Da Saudia Sun Gudanar da taro a nan birnin Tehran, inda suka tattauna kan al-amuran tsaro a yankin. Tashar talabijan ta

Wakilan kasashen Iran, Pakistan Turkiya Da Saudia Sun Gudanar da taro a nan birnin Tehran, inda suka tattauna kan al-amuran tsaro a yankin. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa taron wanda gwamnatin kasar Pakistan ta bada shawarar a gudanar da ita, ta sami amincewar JMI, da sauran kasashen.

Labarin ya kara da cewa skataren majalisar koli na tsaron kasar Iran ne, Wato Janar Mehsen Rizaei ne yake daukar bakwancin taron wanda aka gudanar da shi a safiyar yau litiin.

Fiel Mashal Asim Munir babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Pakistan, Ministan tsaro na kasar Saudia Yerima Khalid bin Salman da daraktan al-amuran leken asiri na kasar Turkiya Ibrahim Lakin duk suna wakiltan kasashensu a wannan taron. Banda haka ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya sami halattan taron. Kafin bakin su gana da shugaban kasa  Dr Masoud Pezeshkiyan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted