Iran Da Oman Na Zurfafa Dangantaka Don Zaman Lafiya da Tsaro

Shugaban kasar Iran, ya jadadda aniyar Jamhuriyar Musulinci ta Iran, na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin da ma dukkanin kasashen Musulmi. A

Shugaban kasar Iran, ya jadadda aniyar Jamhuriyar Musulinci ta Iran, na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin da ma dukkanin kasashen Musulmi.

A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen kasar Oman, Sayyid Badar bin Hamad al-Busaidi a jiya, shugaba Masoud Pezeshkian ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin da ma dukkanin kasashen musulmi.  

Shugaban ya bayyana alakar da ke tsakanin Iran da Oman a matsayin dadaddiyar alakar dogon lokaci, cikin gaskiya da kuma tushen amincewa da juna.

Ya kuma yi tsokaci kan taron da kwamitin hadin gwiwa na tattalin arzikin Iran da Oman zai yi, inda ya ce, ana daukar muhimman matakai don hanzarta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla a baya, da kuma cimma sabbin fahimtar juna da za su amfani kasashen biyu.

Shugaban ya bayyana muhimmiyar rawar da kasar Oman ke takawa a manufofin ketare na Iran, wanda ke mai da hankali kan karfafa alaka da kasashen musulmi da kasashen da ke makwabtaka da ita.

Da yake karin haske kan wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Oman ya mika gaisuwar Sultan Haitham bin Tariq ga Jagoran juyin juya halin Musulunci, shugaban kasa, da al’ummar Iran. Ya kuma yaba da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, inda ya bayyana cewa, an gina ta ne bisa amana da kuma kyakkyawar alaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments