Iran : Mutum 3,375 sukayi shahada a cikin kwanaki 40 na yakin

Hukumar binciken laifuka ta Iran ta ce akalla mutane 3,375 ciki har da daruruwan yara, suka yi shahada a cikin kwanaki 40 na yakin da

Hukumar binciken laifuka ta Iran ta ce akalla mutane 3,375 ciki har da daruruwan yara, suka yi shahada a cikin kwanaki 40 na yakin da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka kaddamar kan kasar.

Abbas Masjedi, shugaban kungiyar likitoci ta Iran, ya fada a ranar Litinin cewa yakin, yakin wanda ya fara a ranar 28 ga Fabrairu, ya kasance cike da wahalhalu, amma shahadar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei da wasu kwamandoji na daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali a cikin al’ummar Iran.

Ya kara da cewa wadanda sukayio shahada sun hada da fararen hula, yara, tsofaffi, da ma’aikata a bangaren gwamnati.

Ya bayyana harin bam din makarantar firamare ta Shajareh Tayyebeh da ke kudancin birnin Minab a matsayin wani lamari mai tayar da hankali, yana mai cewa sama da yara 160 ne suka yi shahada a harin Amurka da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted