Iran : Muna kan tantance bukatun Amurka

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ya yi Karin haske game da tattaunawar da ta wakana tsakankin kasar da Amurka a ranar Juma’a da

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ya yi Karin haske game da tattaunawar da ta wakana tsakankin kasar da Amurka a ranar Juma’a da ta gabata.

Abbas Araghchi, ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRI) tana tantance matsayin Amurka, kafin ya fayyace cewa tattaunawar, idan ta ci gaba, za ta mayar da hankali ne kawai kan shirin nukiliyar Iran.

“Ana nazarin sakamakon tattaunawar ta ranar Juma’a, kuma za a yanke shawara game da ci gaba da tattaunawar,” in ji Mista Araghchi, yana mai bayyana cewa matsayar da bangarorin biyu suka cimma a karshen taron ita ce ci gaba da tattaunawar.

Duk da haka, ya nuna shakku game da halayyen Amurka, yana mai la’akari da ci gaba da sanya wasu takunkumi da matakan soja na Amurka wadanda ya ce suna haifar da shakku game da tattaunawa ta gaskiya.

Da yake magana game da goyon bayan da kasashen yankin suka bayar, ciki har da Turkiyya, Pakistan, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Masar, da Azerbaijan, suka bayar kan tattaunawar Mista Araghchi ya ce: “Za mu ci gaba da shawarwari da su, kamar yadda muke ci gaba da shawarwarinmu da Rasha da China, abokan huldarmu na dabaru, wadanda muka yi musu bayani dalla-dalla; kuma za mu ci gaba da tuntubar su kan halin da ake ciki.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted