Kakakin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa martanin JMI idan an sake far mata da yaki yana iya wucewa zuwa kasashe wajen yammacin Asia.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Burgedia Janar Mohammad Akramnia yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa sojojin kasar a shirye suke fiye da kafin yakin kwanaki 40.
Yace sojojin Iran sun kara kyautata garkuwan makaman makiya da kuma farfi nisan da harensu zasu iya kaiwa. Banda haka karfin makamai da kuma wurare da zasu fada duk a shirye suka.
Dangane da umurnin jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Mujtaba Khaminaei, na cewa su maida martani ba tare da kula da wani yanki ba, Akramnia y ace a yake yaken da suka gabata, mafi yawan hare harensu sun takaita ne a kan sansanonin sojoji da makaman makiya a kuma cikin kasashen Asia. Amma a wannan karon, idan makiya sun takali yaki da Iran, muna iya kai hare hare kan kasashe wajen yankin yammacin Asiya.
Yace idan makiya sun sake farwa kasar Iran da yaki, kadaroyi da rayukan sojojin makiya suna cikin hatsari a cikin kasashen yammacin Asiya ko wajensa, suna cikin hatsari a duk inda makaman JMI zasu iya kaiwa. Daga karshe yace, yakin, a wannan karon zai yi tsawo fiye da yanda ake tsammani.