Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran.
Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba.
Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu.
Akan barazanar da wasu kasashe suke yi wa kungiyar ta “Brics kuwa Ahmadiyan ya ce; Hakan yana nuni ne da zurfin damuwa akan abinda Brics din za ta iya yi domin zama kungiya mai karfi a nan gaba a fagagen siyasa, tattalin arziki, da kuma al’adu.