Majalisar tsarin mulkin kasar Iran ta tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli, wanda ya kai ga nasara Masoud Pezeshkian.
“Majalisar tsarin mulki ta amince da ingancin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa karo na 14,” in ji kakakinta Hadi Tahan Nazif a ranar Lahadi.
Ya kara da cewa an sanar da ma’aikatar harkokin cikin gida, hukumar da ke kula da gudanar da zaben a hukumance kan lamarin.
Ya kara da cewa babu wani dan takara da ya kai koke ko kuma ya kai rahoton wani cin zarafi ga majalisar tsarin mulki, mai wakilai 12 da ke sa ido kan zaben.
Majalisar kuma ba ta samu wani muhimmin rahoto daga jama’a da za su yi tasiri a sakamakon zaben ba, in ji shi.
Masoud Pezeshkian, Kwararen likitan zuciya ne ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Juma’a data gabata.
Ya samu kuri’u sama da miliyan 16 a kan tsohon mai shiga tsakani na nukiliyar kasar Saeed Jalili, wanda ya samu sama da miliyan 13 daga cikin sama da kuri’u miliyan 30 da aka kada.