Majalidar Dokokin Iran ta amince da jerin sunayen ministocin da sabon shugaban kasar Massoud Pezehkian, ya gabatar a matsayin mambobin gwamnatinsa.
A jiya ne majalisar ta kawo karshen muhawarar da aka kwashe kwanaki anayi inda daga karshe aka amince da dukkan ministoci 19 da shugaba Pezeshkian ya nada.
A zaman na kwanaki hudu ana tattaunawa mai zafi, ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da dukkan ministocin da sabon shugaban kasar ya gabatar.
Pezeshkian ya mika jerin sunayen ministocin da ya gabatar wa majalisar dokokin kasar domin neman amincewa da su a ranar 11 ga watan Agusta, kwanaki 12 bayan rantsar da shi.
‘Yan majalisar dai sun tattauna kan cancanta da shirye-shiryen wadanda aka nada a matsayin ministoci.
Daga cikin ministocin da suka samu sahalewar majalisar har da Abbas Aragchi, wanda zai maye gurbin Hossein Amir-Abdollahian a matsayin sabon ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Gabanin kada kuri’a a ranar Laraba, shugaba Pezeshkian ya yi jawabi ga majalisar dokokin kasar inda ya bukace su da su amince da sunayen ministocinsa yayin da ya kuma yi kira ga “hadin.”
Sabbin ministocin zamu maye gurbin na tsohon shugaban kasar Shahid Ebrahim Ra’isi, wanda ya rasu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayun da ya gabata tare da wasu mukarabansa.