Iran, ta bayyana kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a Gaza ba shi da misali a tarihi.
Wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya fada a jiya Talata cewa : Sojojin da ake kira masu”dabi’a” sun yi wa Falasdinawa kusan 41,000 kisan gilla, musamman mata da kananan yara.
Hakan a cewar wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya : Laifukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata ba a taba ganin irinsu ba.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa, tun daga farkon yakin Gaza a farkon watan Oktoban 2023, adadin shahidai a zirin Gaza ya kai 40,500 sannan adadin wadanda suka jikkata 92,401, wanda kashi 33% yara ne, kashi 8.6% tsofaffi ne sannan 18.4% mata ne.