A Iran Kirayen kirayen daukar fansa kisan Ayatollah Ali Khamene’I na dada wanzuwa.
Kalamman Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC na a cikin na baya bayan dake kiran daukar fasan.
Rear Admiral Ali Azmaei ya gargadi Amurka da gwamnatin sahyoniya cewa daukar fansar shahadar marigayi Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyed Ali Khamenei ya kusa, yana mai alkawarin cewa Sojojin Iran za su ci gaba da bin tafarkinsa.
A cikin wani sako da aka fitar yau Asabar, Kwamandan ya yi wa marigayi Jagoran godiya, yana mai bayyana shi a matsayin wata alama ta hakuri, fahimta da juriya wacce gadonta da manufofinta za su ci gaba da zaburar da al’ummar Iran da al’ummar Musulunci.
Kwamandan ya ce daukar fansar ga “Amurka da “gwamnatin sahyoniya ba ta da nisa” saboda shahadar Jagoran juyin juya halin Musulunci.
Ya yi Allah wadai da kisan Ayatollah Khamenei, yana mai cewa “mafi sharrin masu laifi” ne suka aikata hakan saboda tsoron tasirinsa, jajircewarsa mara misaltuwa da kuma jagorancinsa mai tasiri.
Bayanin kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ya zo ne a daidai lokacin da daruruwan dubban masu makoki suka taru a Imam Khomeini Musalla na Tehran don bikin bankwana da Jagoran juyin juya halin Musulunci.