A ci gaba da tunawa da cika shekaru biyar da shahadar Laftanar Janar Qasem Soleimani, Iran na gudanar da wani taro na musamman karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Za a gudanar da taron ne a safiyar yau Laraba a Husainiyyah Imam Khumaini da ke birnin Tehran.
An tsara Iyalan Shahidai Soleimani, da mukarabansa, da kuma wadanda harin ta’addancin da Amurka ta kai musu lokacin mulkin tsohon shugaba Donald Trump su za su gana da Jagoran.
Haka kuma bikin zai samu halartar dimbin jama’a, da suka hada da iyalan shahidai, da mayaka, da kuma manyan masu fafutuka na gwagwarmayar. Za su halarci wurin jawabin Ayatullah Khamenei.
Marigayi Janar Shahid Qassem Soleimani, kwamandan dakarun Rundunar Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) na Iran, ya kasance wata alama ta tsayin daka da kuma abin alfahari na kasa ga Iraniyawa da dama.
An kashe Janar Soleimani, kwamandan dakarun Quds na Iran tare da Abu Mahdi al-Muhandis, babban kwamandan rundinar Hashdu Sha’abi ta Iraki na biyu tare da abokansu sun yi shahada a harin jirgin yakin Amurka a ranar 3 ga Janairu, 2020.