Search
Close this search box.

Iran : Jagora Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Game Da Mummunar Fashewa A Mahakar Ma’adanai

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalen mamatan ifti’la’in fashewar data auku a mahakar

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalen mamatan ifti’la’in fashewar data auku a mahakar ma’adanai ta a garin Tabas da ke gabashin kasar.

 Jagoran a cikin sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan ya jaddada; bukatar tura duk abinda akebukata na samar da agaji ga ma’aikatan da abin ya shafa ko kuma suka makale a cikin mahakar.

Gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a lamarin da ya faru da misalin a daren Asabar.

Tunda farko kafofin yada labaren kasar sun ce akalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu kuma wasu da dama sun jikkata a lamarin.

An ruwaito cewa fashewar sinadarin methane ce ta afku a wasu sassa biyu na wurin hakar ma’adinan a garin Tabas mai tazarar kilomita 540 a kudu maso gabashin Tehran, babban birnin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments