Iran : IRGC Ta Kaddamar Da Wani Atisaye A Kusa Da Cibiyar Nukiliyar Natanz

Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da wani gagarumin atisayen soji a lardin Isfahan da ke tsakiyar kasar. Matakin farko

Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da wani gagarumin atisayen soji a lardin Isfahan da ke tsakiyar kasar.

Matakin farko na atisayen mai lamba Eqtedar 1403, ya fara ne yau Talata a kewayen cibiyar sarrafa Uranium ta Natanz bisa umarnin Birgediya Janar Qader Rahimzadeh, kwamandan sansanin tsaron saman kasar na Khatam al-Anbia.

A wannan lokaci na atisayen soji, rundunonin tsaron sama na IRGC na ba da cikakkiyar kariya ga tashar nukiliyar Shahid Ahmadi Roshan, wacce aka fi sani da Natanz, daga duk wata barazana.

Sojojin kasar Iran na gudanar da atisaye na yau da kullum domin gwada makamansu da kayan aikinsu da kuma tantance shirinsu na yaki.

Jami’an kasar sun sha nanata cewa kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen karfafa karfin sojinta da ke da nufin kare kai daga sabbin barazana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments