Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen kiwon dabbobi.
Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.”
Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa.
Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar samar da abinci mafi girma a cikin wannan yankin.