Kasashen Iran da kuma Iraki sun kudiri anniyar karfafa alaka ta fuskar makamashi.
A ganawar da suka yi a birnin Bagadaza, kasashen biyu sun jaddada fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin mai da iskar gas, inda kasar Irakin ta bayyana matukar sha’awar yin hadin gwiwa a fannin fasaha da zuba jari da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Taron ya yi nuni da karfafa huldar dabarun samar da makamashi tsakanin kasashe biyu masu makwabtaka da juna.
Mataimakin firaministan kasar Iraki mai kula da harkokin makamashi Hayan Abdul-Ghani Al-Sawad ya bayyana cewa, Iraki na ci gaba da gudanar da ayyukan da ke da nufin cimma dogaro da kai wajen samar da albarkatun man fetur.
Ya jaddada aniyar Bagadaza na fadada hadin gwiwar fasaha da kuma jawo hannun jarin Iran a bangaren makamashi na Iraki.
Iraki na da burin rage dogaro da man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje kuma tana kallon Iran a matsayin babbar abokiyar huldar cimma wannan buri saboda ci gaban da take da shi na tace man.