Esma’il Khatib: Isra’ila Na Fuskantar Manyan Ayyukan Leken Asiri Daga Iran

Ministan ayyukan leken asiri na kasar Iran Esma’il Khatib ya bayyana cewa Isra’ila na fuskantar ayyukan leken asiri mafi muni a tarihin samauwar haramtacciyar kasar,

Ministan ayyukan leken asiri na kasar Iran Esma’il Khatib ya bayyana cewa Isra’ila na fuskantar ayyukan leken asiri mafi muni a tarihin samauwar haramtacciyar kasar, kuma a halin yanzun Jami’an tsaron HKI da dama suna aikin leken asiriwa wa Iran, musamman bayan da gwamnatin yahudawan ta bada sanarwan kama wani sojan rundunar sama ta kasar saboda aiki leken asiri wa Iran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Khatib yana fadar haka a jiya Asabar a wani ziyarar aiki da ya kai lardin Kokulue Boye Ahmad a kudancin kasar.

Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun bada sanarwan cewa, sun tabbatar da cewa laifin aikin leken asiri wa kasar Iran kan wani sojan sama na kasar dan shekara 22 a duniya, wanda ya aikawa kasar Iran bayanan soje masu muhimman, wadanda kuma suka shafi makaman nukliyar haramtacciyar kasar.

Khatib ya kara da cewa wannan al-amarin ya tabbatar da irin karfin da JMI take da shi a ayyukan leken asiri a yanking abas ta tsakiya. Kuma wannan kwarewar yana daukaka a matsayinta a yankin da kuma duniya gaba daya. Ministan ya kara jaddada cewa duniya tana sauyawa kuma JMI na daga cikin kasashen da sami ci gaban a zo a gani a yankin da da kuma duniya.

Daga karshen ministan ayyukan leken asiri na Iran ya ce yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata tsakanin JMI da Amurka da kuma Isra’ila ya bayyana wani bangare na irin karfin da JMI take da su a fagen makamai da kuma yakin na’urori da harnyoyi na zamani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments