Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa samuwar HKI a gabas ta tsakiya it ace barazana mafi girma ga zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma duniyar gaba daya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Naseer Kan’ani yana fadar haka a jawabinsa na mako mako a jiya Litinin.
Kan’ani ya kara da cewa akwai labaran da suke yaduwa kan cewa gwamnatin HKI zata ci farwa kasar Lebanon da yaki. Ya kuma kara da cewa sojoji da sauran jami’an tsaro a kasar Lebanon suna da hakkin kare kansu daga duk wani harin da sojojin HKI zasu kaiwa kasar. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya musamman MDD su yi aikinsu na tabbatar da zaman lafiya a duniya musamman a yankin gabas ta tsakiya.