Majid Akhvan kakakin hukumar kula da zirga-zirgan jiragen sama ta kasar iran ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama na kasar iran basu suke ko daya daga cikin tafiye tafiyensu zuwa kasashen waje ba suna ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda aka tsara
Haka zalika hukumar jiragen sama ta sanar da cewa ba su samu sakwanni daga humomin jiragen sama a hukumance ba na kasashen turkiya da Azarbaijan ko iraki da suka dakatar da zirga -zirgar jiragen sama zuwa Istanbul, baku, ko Najaf ba, kamfanin jiragen saman sun ce su ci gaba da amfani da wadannan hanyoyin, sai dai idan sun samu wasu bayanai na daban
Sakatare baitul malin Amurka Scott Bessent ya fadi cewa zaa dakatar da dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar iran daga zirga –zirgar kasa da kasa daga ranar 23 ga watan satumba, kuma yayi gargadin cewa duk wata kasa da ta bada mai ga jiragen iran ko kuma wasu kamfanoni da suka yi aiki da ita to za su fuskanci takunkumin Amurka
Yace Amurka ta sanar cewa a ranar 8 ga watan satumba ta sanya takunkumi ga kamfanoni 36 dake da alaka da bangaren kula da zirga zirgan jiragen sama na kasar iran, da suka hada da dukkan sauran kamfanin jiragen sama na yan kasuwa da kuma kamfanonin kasashen waje dake aiki da su,
sai dai wannan takunkumin yana zuwa ne sakamakon kashi da amurka ta sha a bangaren soji da yakin da ta kaddamar kan kasar iran