Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Venezuela da mutanen kasar zasu kare diyaucin kasar da kuma zaluncin gwamnatin Amurka, a kokarin da Trump yake na kwace shugabancin kasar daga hannun Shugaba Madoro.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a taron Vedio Confrence da jakadan kasar Iran a birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a jiya Litinin.
Aragchi ya yabawa jakadan da sauran Jami’an diblomasiyya na JMI da suke birnin Caracas suke kuma aiwatar da ayyukansu na jakadanci kamar yadda ya dace. Dangane da jita jitan da ke yaduwa kan cewa Iran ta janye jami’an diblomasiyyar kasar daga birnin Caracas sannan ta rufe wasu kamfanonin kasar a Venezuela ba gaskiya bane. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baqa’ii ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ne ba. Kuma dukkan jami’an diblomasia da kuma kamfanoni daban-daban na kasar Iran da suke aiki a kasar Venezuela suna gudanar da ayyukansu ba tare da kula da kawanyar da sojojin Amurka suka yiwa kasar ba. Baghaei yace abinda ke faruwa a kasar Venezuela wano kalu bale ne ga kasashen duniya musamman MDD wacce take da hakkin kare wadannan kasashe daga azzaluman kasashe kamar Amurka, a bisa tsarin zamantakewa na kasa da kasa.