Babban ahfsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manji Janar Abdurrahin Musawi ya bayyana cewa sojojin kasarsa sun sauya tsarinsu na tsaron kasar, wanda kuma shi ne a halin yanzu idan makiya kasar sun takali kasar da yaki ko menena karancinsa zai jawo martani mai tsanani kansu.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa wannan bayanin ya nuna yadda sojojin kasar suka kara tsanaanta zaman dar dar da ake ciki a yankin a dai dai lokacinda sojojin Amurka suke cicirindo a gewayen kasar Iran.
Iran ta jadda cewa tana shirin maida martani da gaggawa don samun nasara a kan Amurka da kawayenta a duk wani yakin da zasu fara.
Janar Musawi ya bayyana cewa maganar rikicin baya bayan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimani 3000 bata kare ba, kuma Iran zata dauki duk wata dama da ta samu da takalar makiya don ta dauki fansa da gaggawa kan makiyanta. Yace duniya zata ga sabuwar faskar kasar Iran a duk wani yaki da zai hadata da makiyanta.
Ya kammala da cewa irin wannan halin babu wani ba’americe da zai tsira daga hannummu.